Isa ga babban shafi
Zambia

An sake zaben Lungu a Zambia

Sabon shugaban Zambia, Edgar Lungu
Sabon shugaban Zambia, Edgar Lungu DR
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Hukumar Zabe a kasar Zambia ta bayyana shugaban kasa Edgar Lungu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a kasar, sai dai abokin takararsa Hakainde Hichelema ya ce zai je kotu don kalubalantar sakamakon.

Talla

Edgar Lungu ya lashe zaben ne da sama da kashi 50 cikin 100 na yawan kuri’u da aka kada,

An gudanar da zaben ne a ranar Alhamis kuma Lungu ya samu rinjayen kuri’u fiye da abokin hamayarsa Hakainde Hichilema.

Sakamakon na karshe na cewa lungu ya samu kuri’u miliyan 1.86, yayin da Hichilema ke da miliyan 1.66.

Jami’iyyar UNDP ta Hichilema ta yi zargin an yi magudi a zaben, musamman lokacin da aka dauka kafin fitar da samakon karshe.

Kafin gudanar da wannan zabe an samu rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasar kasar, abin da ya kai ga kashe mutane uku.

Jam’iyyar adawa ta UPND ta ce za ta kalubalanci zaben a shari’ance domin suna da tabbacin cewa magudi aka yi.

Lungu dai ya shafe watanni 19 akan karagamar Mulki bayan karbe iko kasar a wani zaben da ya doke Hichilema da kuri’u dubu ashirin da takwas sakamakon mutuwar shugaba Michael Sata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.