Guinea Bissau

ECOWAS zata fice daga Guinea Bissau

Dakarun wanzar da zaman lafiya na ECOWAS
Dakarun wanzar da zaman lafiya na ECOWAS dailynewsegypt.com

Kungiyar ECOWAS tace sojojin ta da suka samar da tsaro a kasar Guinea Bissau mai fama da juyin mulki zasu fice daga kasar nan da shekara guda. 

Talla

Shugaban gudanarwar kungiyar Marcel Alain De Souza ya ce babu dalilin ci gaba da zaman dakarun ECOWAS a kasar.

Shekaru 4 kenan dakarun na zaune a Guinea Bissau don tabbatar da cewa an samu tabbataccen tsaro a kasar.

De Souza yace cikin watanni shida masu zuwa sojojin kungiyar zasu cigaba da horar da takwarorin su na Guniea Bissau dan inganta tsaro a cikin gida.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.