Isa ga babban shafi
Zambia

Za a jinkirta rantsar da Edgar Lungu

Shugaba Edgar Lungu na Zambia
Shugaba Edgar Lungu na Zambia GIANLUIGI GUERCIA / AFP
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 Minti

Shugaban Kasar Zambia Edgar Lungu ya sanar da cewar za a jinkirta rantsar da shi wa’adi na biyu sakamakon karar da abokin takarar sa Hakainde Hichilema ya shigar a kotu saboda zargin magudi.

Talla

Dokar zaben kasar tace ba za a rantsar da wanda ya samu nasara ba har sai kotu ta kamala tantance sahihancin zaben cikin makwanni biyu.

'Yan Sanda sun sanar da kama mutane 150 da suka gudanar da zanga zanga dan nuna adawar su da sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.