Isa ga babban shafi
Zambia

Hakainde Hichilema ya ruga kotu

Hakainde Hichildma shugaban yan adawa a kasar Zambia
Hakainde Hichildma shugaban yan adawa a kasar Zambia REUTERS/Rogan Ward
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Yan Sanda a kasar Zambia na cigaba da sa ido dama tabbatar da tsaro a wasu wurare na kasar ,wani mataki na gujewa tashin hankali ,a makon da ya gabata dai ne suka sanar da kama mutane 150 da suka gudanar da zanga zanga dan nuna adawar su da sakamakon zaben.

Talla

Shugaban yan adawa Hakainde Hichilema ya shigar da kara zuwa kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar na cewa an tafka magudi a zaben shugabancin kasar,Hichilema mai shekaru 54 ya na neman kotu ta soke sakamakon zaben.
Sai dai Shugaban Kasar Zambia Edgar Lungu ya sanar da cewar za’a jinkirta rantsar da shi wa’adi na biyu sakamakon karar da abokin takarar sa Hakainde Hichilema ya shigar a kotu saboda zargin magudi.

Dokar zaben kasar tace ba za’a rantsar da wanda ya samu nasara ba har sai kotu ta kamala tantance sahihancin zaben cikin makwanni biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.