Chad

Kotu ta yi watsi da zargin bacewar Sojoji a Chadi

Shugaba Idris Deby na Chadi
Shugaba Idris Deby na Chadi REUTERS/Tiksa Negeri

Kotu a kasar Chadi ta yi watsi da zargin da ake yi na bacewar wasu sojojin kasar da dama a lokacin zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan Afrilun da ya gabata.

Talla

Da farko dai jam’iyyun adawa da kuma wasu kungiyoyin fararen hula sun yi zargin cewa sojoji fiye da 20 ne aka kama kuma bisa ga dukkan alamu an kashe su saboda sun ki jefa wa shugaba Idris Deby Kuri’unsu.

To sai dai bayan wani bincike dangane da zargin, bangaren shara’a ya yi watsi da zargin saboda rashin hujja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI