Zika

Najeriya na fuskantar barazanar Zika

Har yanzu masana na binciken gano rigakafin cutar Zika
Har yanzu masana na binciken gano rigakafin cutar Zika Scott Olson/Getty Images/AFP

Wani binciken masana kiwon lafiya ya nuna cewar kashi daya bisa uku na al’ummar duniya sama da biliyan biyu da rabi wadanda ke zama a Afirka da Asia da kuma Yankin Pacific na fuskantar barazanar kamuwa da cutar Zika.

Talla

Binciken ya nuna cewar al’umomin da ke kasashen India da China da Indonesia da Najeriya da Pakistan da Bangladesh ke fuskantar  barazanar kamuwa da cutar Zika.

Binciken ya jefa alamar tambaya game da kariyar da al’ummar wadannan kasashen ke da ita daga cizon sauron da ke yada cutar Zika.

Tuni dai aka ruwaito bullar Zika a Afrika da Asia, kuma binciken ya ce babu wanda ya san girman yaduwar Cutar da har mutane da za su yi gaggawar daukar matakan kariya.

Zika na yaduwa ne ta hanyar cizon sauro, Kuma cutar na yaduwa idan wani sauro a wata kasa ya ci ji mutumin da ke dauke da Zika.

An gudanar da binciken ne ta yin amfani da tarihin matafiya da yanayi da yadda sauro ke yaduwa a kasashen Afrika da Asia.

Sama da mutane miliyan guda da rabi ke dauke da cutar Zika a Brazil kuma sama da  jarirai 1600 aka Haifa da nakasa.

Matan da suka kamu da Zika na haihuwar yara masu karamin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.