Gabon

Ping ya shigar da kara a kotu kan zaben Gabon

Shugaban 'yan adawar Gabon Jean Ping
Shugaban 'yan adawar Gabon Jean Ping REUTERS/Noor Khamis/File Photo

Dan takarar shugabancin kasar Gabon na jam’iyar adawa da ya sha kayi a zaben da aka gudanar, ya shigar da kara a gaban kotun tsarin mulki don kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa shugaba mai ci Ali Bongo Odimba nasara. 

Talla

Kotun na da makwanni biyu kafin ta yanke hukunci kan karar da Jean Ping ya shigar in da daga nan ne za ta sanar da sunan wanda ya yi nasara a zaben wanda ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen kasar.

Tazarar kuri’u dubu sittin ne a tsakanin Ali Bongo da  Ping kamar yadda  sakamakon zaben na ranar 27 ga watan Augusta ya nuna.
 

An samu barkewar rikice-rikice a wasu biranen kasar bayan da hukuamar zabe ta sanar da sakamakon, abinda ya haddasa asarar rayuka da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.