Isa ga babban shafi
Tanzania

Girgizar kasa ta kashe mutane da dama a Tanzania

Mutane 16 sun rasu a girgizar kasar da ta afka wa Tanzania
Mutane 16 sun rasu a girgizar kasar da ta afka wa Tanzania REUTERS/Navesh Chitrakar
Minti 1

A kalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu, in da kuma 253 suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 5.7 da ta afka wa yankin arewa maso yammacin Tanzania.

Talla

Shugaban kasar, John Magufuli ya bayyana damuwarsa kan ibtila’in, wanda ya faru a kusa da kogin Victoria da kuma kan iyakokin Uganda da Rwanda.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa, fiye da gidaje 800 girgizar kasar ta rusa, yayin da ma’aikatan agaji ke ci gaba da neman masu sauran kwana da lamarin ya ritsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.