Isa ga babban shafi
Zambia

Lungu ya bukaci hadin kan 'yan kasar Zambia

Shugaban Zambia Edgar Lungu yayin bikin rantsuwar sa a Lusaka
Shugaban Zambia Edgar Lungu yayin bikin rantsuwar sa a Lusaka
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya bukaci hadin kan daukacin ‘yan kasar, yayin da ya gabatar da jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar.

Talla

Lungu ya ce a yanzu gwamnatinsa zata maida hankali ne kan farfado da tattalin arzikin kasar da ke samun koma baya.

Sai dai kuma abokin hamayyar shugaba Lungu, wato Hakainde Hichilema wanda ya gaza samun nasara dakatar da rantsuwar a kotu, ya ce rantsar da Lungu ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Kasar Zambia ta yi suna game da rashin samun rikicin siyasa, amma a zaben shugaban kasar da aka kammala an samu tashe tashen hankula tsakanin magoya bayan shugaban mai ci Edgar Lungu da kuma na abokin hamayyarsa Hakainde Hichilema.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.