Isa ga babban shafi
Hungary

Al’ummar kasar Hungary na zaben jin ra’ayi kan ‘yan gudun hijra

Yan gudun hijra a artabu tsakaninsu da yan sandan kasar Hungary a kokarin shiga kasar ta karfi.
Yan gudun hijra a artabu tsakaninsu da yan sandan kasar Hungary a kokarin shiga kasar ta karfi. Reuters/路透社
Zubin rubutu: Ramatu Garba Baba
Minti 2

Mutane da dama sun fito a yau lahadi don kada kuri’unsu a zaben raba gardama akan  karbar ‘Yan gudun hijra bisa tsarin Kungiyar Tarrayar Turai na raba ‘yan gudun hijrar a tsakanin kasashe dake mambobin kungiyar.

Talla

Akalla ‘yan gudun hijra dubu daya da dari uku ya kamata Hungary ta baiwa mafaka sai dai da dama daga cikin al’ummar kasar na adawa da tsarin, hakazalika Firaiyi Ministan kasar Victor Orban.

Tun lokacin da aka soma samun matsalar kwararar ‘yan gudun hijra a Turai, kasar Hungary ta rufe kan iyakokinta da Croatia a wani mataki na hana bakin shiga kasar.

Sabanin dake a tsakanin kasashe mambobin Kungiyar EU ya jefa tsare tsaren Tarrayar Turai kan ‘yan gudun hijra cikin mawuyacin hali.

Dubban ‘yan gudun hijra da yaki ko yunwa ya tilastawa barin kasashensu ne ke galabaita akan iyakokin kasashen Turai ganin yadda da dama daga cikin wadannan kasashen ke kin basu mafaka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.