Isa ga babban shafi
Gabon

Ma'aikatar leken asirin Gabon ta bankado hirar tawagar EU

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba RFI/Carine Frenk

Hukumar leken asirin kasar Gabon ta saurari hirarrakin mambobin tawagar tarayyar turai da suka je aikin sa ido a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 27 ga watan jiya.

Talla

Wata jaridar kasar Faransa mai suna ‘Le Journal du Dimanche’ ta bankado labarin, a cikin hirarrakin 20 da jaridar ta bayyana wandanda aka nada a asirce.

Cikin hirar dai an ji mambobin tawagar na bayyana shakka kan sakamakon zaben da yaba Ali Bango nasara. Haka kuma suna zaton shugaba mai ci ya shirya magudin zabe.

Kasar Gabon ce dai ta gayyaci tawagar sa ido daga Tarayyar Turai kan zaben shugaban kasar da aka shirya sai dai sun soki yanayin zaben sosai da kuma aikin tattara sakamakon zaben da suka ce su tattare da kura.

Sai dai tuni kasar Gabon ta yi watsi da wannan batu ta muryar ministan sadarwar kasar Alain Claude Bilie, inda ya bayyana labarin a matsayin tabarmar kunya ce aka nade ta da hauka don a boye shigar tawagar tarayyar Turan ne cikin harakar zaben kasar ta Gabon.

Tun farko dai shugabannin kasar Gabon sun samu sabani da tawagar tarayyar Turai, da ta soki shirye-shiryen zaben, a yayin da suke kallonsu a matsayin wandanda suka marawa dan takara adawa baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.