Habasha ta kaddamar da layin jirgi mai nisan kilomita 750
Wallafawa ranar:
Habasha ta kaddamar da wani layin jirgin kasa mai nisan kilomita 750 wanda zai hada kasar da Djibouti.
Talla
Kakakin kamfanin jiragen, Dereje Tefera, ya ce wani kamfanin China ne ya gina layin jirgin na zamani a kan Dala biliyan 4 wanda ake saran saukaka harkokin sufuri tsakanin kasashen biyu da kuma kaucewa gurbata muhalli.
Jami’in ya kuma ce jiragen da za su yi aiki tsakanin kasashen za su taimakawa manoma wajen fitar da amfanin gonakin su zuwa kasuwanni a farashi mai sauki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu