Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Tarayya ta gayyaci Buhari kan Tattalin arziki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Majalisar Dattijai da ta wakilan Tarayya sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a gabansu domin gabatar da jawabi kan dubarun da gwamnatin shi ke bi na fitar da Najeriya daga kangin matsalar tattalin arziki.

Talla

Majalisun biyu na bukatar cikakken bayani ne daga shugaba Buhari akan matakan da gwamnatin shi ke dauka domin magance matsalolin tattalin arzikin da Najeriya ta shiga, musamman faduwar darajar Naira da ya haifar da tsadar kayayyaki da kuma yadda matsalar ta shafi rasa aikin yi.

Tun da farko Majalisar Dattijai ta amince da wani daftari mai kunshe da hanyoyin bunkasa ayyukan noma tare da taimakawa Najeriya karkatar da tattalin arzikinta daga dogaro da arziki fetir.

Zuwa yanzu dai fadar Shugaban kasa ba ta amsa cewa ko Buhari zai bayyana a gaban 'Yan Majalisun ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.