Najeriya

Kungiyar Lauyoyi ta yi allawadai da farmakin da aka kai wa Alkalai

Hukumar 'Yan sandan Farin kaya ta DSS ta ce zata ci gaba da bincike akan Alkalan Najeriya
Hukumar 'Yan sandan Farin kaya ta DSS ta ce zata ci gaba da bincike akan Alkalan Najeriya guardian

Kungiyar lauyoyi a Najeriya ta soki dirar mikiyar da hukumar ‘Yan sandan farin kaya ta yi wa gidajen manyan alkalai a sassan kasar.

Talla

A lokacin da ya ke mayar da martani Shugaban kungiyar Abubakar Mahmud ya ce sun yi allawadai da farmakin da ‘Yan sandan na farin kaya suka kai wa alkalan na Najeriya.

Mista Mahmud ya ce a mulkin dimukuradiya ba za su amince da irin wannan yanayin ba inda ‘Yan sanda za su abkawa gidajen Alkalansu na kotun koli da na babbar kotu.

Hukumar ‘Yan sandan na farin kaya dai ta ce ta kwato miliyoyan daloli a gidajen alkalan wadanda ta ke zargi da laifin karbar cin hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.