Isa ga babban shafi
Najeriya

Chibok : Buhari ya gindaya wa Boko Haram Sharadi

Kungiyar BringBackOurGirls (#BBOG) da ke fafutikar ganin an sako 'yan matan Chibok
Kungiyar BringBackOurGirls (#BBOG) da ke fafutikar ganin an sako 'yan matan Chibok REUTERS
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin shi za ta ci gaba da tattaunawa da Boko Haram kan batun sako sauran ‘Yan matan Chibok amma sai idan kungiyar ta amince kungiyar agaji ta Red Cross ta shiga tsakani.

Talla

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina ya fitar, Buhari ya yi jinjina ga kungiyar agaji ta Red Cross kan rawar da ta taka wajen kubutar da ‘yan Matan Chibok 21 daga cikin sama da 200 da Boko Haram ke garkuwa da su.

Buhari ya gana ne da Shugaban kungiyar Red Cross Peter Maurer a fadar shi, kuma sanarwar ta ce shugaban ya ce za su ci gaba da tattaunawa da Boko Haram amma da sharadi idan kungiyar za ta amince da wakilcin kungiyoyin agaji na duniya kamar Red Cross.

A watan Afrilun 2014 ne Boko Haram ta sace ‘Yan Makarantar Sakandaren garin Chibok sama da 200, kuma a makon jiya ne aka yi nasarar kubutar da 21 tare da taimakon kungiyar agaji ta Red Cross.

Shugaban kungiyar Red Cross ya yi alkawalin taimakawa Najeriya domin ceto sauran ‘yan matan tare da ci gaba da bayar da gudunmuwa ga miliyoyan ‘Yan gudun hijirar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.