Masar

An zartas da dauri na shekaru 20 kan Hambararren Shugaban Masar Mohammed Morsi

Hambararren Shugaban Masar Mohamed Morsi
Hambararren Shugaban Masar Mohamed Morsi AFP PHOTO / STR

Wata Kotun daukaka kara dake kasar Masar ta zartas da hukuncin dauri na tsawo shekaru 20 kan hambararren shugaban kasar Mohamed Morsi, hukunci irinsa na farko tun bayn hambarar da mulkin sa.

Talla

Majiyoyin samun labaran Kotu sun bayyana cewa kotun daukaka karar ta kuma amince da hukuncin da aka zartas a kan wasu na hannun daman hambararren shugaban su takwas.

Bakwai daga cikin su za su yi zama gidan kaso na tsawon shekaru 20, yayin da mutun daya zai yi zama na tsawon shekaru 10 a gidan yari.

A watan hudu na bara aka tuhumi tsohon shugaban da laifin  hannu wajen kisan da aka samu yayin wata zanga-zanga a harabar fadar shugaban kasa a lokacin da yake rike da madafun iko.

Tun kawar da Gwamnatin sa ake tuhumar sa da aikata laifuka barkatai a zamanin sa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.