Somalia

Shirin tsagaita wuta ya rushe bayan fadan da ya hallaka mutane 19

Sabon fada a garin Puntland ya yi sanadiyar rayukan mutane 19.
Sabon fada a garin Puntland ya yi sanadiyar rayukan mutane 19. REUTERS/Abdiqani Hassan

Fadan da aka gwabza da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19 ya rusa yarjejeniyar  zaman lafiya da aka kulla a  tsakanin wasu Yankunan kasar Somalia biyu masu cin gashin kan su

Talla

Rahotanni sun ce an fafata a garin Galkayo tsakanin dakarun Galmudug da Puntland mako guda bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya.

A karkashin yarjejeniyar da Dubai ta jagoran ta, wanda bangarorin biyu suka amince da shi, kowanne yanki zai janye sojojin sa daga inda ake rikicin.

Magajin Garin Galkayo, Hirsu Yusuf Barre ya bayyana kaduwar su da kutsawan dakarun Puntland garin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.