Faransa-Mali

Yan ta’adda ne suka kashe sojin Faransa a Mali

Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian.
Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian. Europe1

Hukumomin kasar Faransa sun tabbatar da cewar harin ‘yan ta’adda ne ya yi sanadiyar kashe daya daga cikin sojojin ta dake aikin samar da zaman lafiya a Mali.

Talla

Ministan Tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya tabbatar da kashe sojan mai suna Fabien Jacq a wani hari da Yan Tawayen Mali suka kaiwa dakarun dake aiki a Arewacin kasar.

Arewacin Mali na daya daga cikin yankunan dake fama da tashin hankali sakamakon hare harenda kungiyar Yan Tawayen Abzinawa da ta Ansar Dine suka kaddamar.

Kungiyar Ansar Dine ta dauki alhakin kai harin da ya hallaka sojan na Faransa, amma gwamnatin Faransa tace bata da tabbacin haka.

A makon jiya an ruwaito shugaban mabiya addinin Muslunci a Mali na bayyana cewar Yan Tawayen sun sanar da shirin tsagaita wuta amma daga bisani Yan Tawayen sun ce ba haka abin yake ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.