Isa ga babban shafi
Malawi

Kotu ta hukunta mutumin da ya yi lalata mata fiye da 100

Eric Aniva dan kasar Malawi da aka daure sakamakon yin lalata da mata fiye da 100
Eric Aniva dan kasar Malawi da aka daure sakamakon yin lalata da mata fiye da 100
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Wata Kotu a kasar Malawi ta yankewa wani mutum mai suna Eric Aniva, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu, bayan ta same shi da laifin lalata da mata fiye da dari, alhalin ya san ya na dauke da kwayar cutar HIV.  

Talla

Kotun ta yanke hukuncin ne, bayan samun mutumin da ake yiwa lakabi da kura, bayan an cafke shi sakamakon tabbatar da cewa ya yi lalata da matan da sunan tsaftacesu bisa al'ada.

Eric kara da bayanin cewa ya yi hakan ne da amincewar iyaye ko dangin matan da ke son a tsabtace ‘ya’yan nasu.

Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ne ya bada izinin a cafke Eric, a kuma hukunta shi daidai da nauyin laifinsa.

Wannan al’amari dai ya ja hankalin kasashen duniya inda aka yi ta tafka muhawara a ciki da wajen kasar, akwai kuma wasu da ke ganin ya kamata gwamnatin Malawi ta soke wannan mummunar al'ada.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.