Isa ga babban shafi
Faransa-Africa

Taron kasashen masu amfani da Faransanci

Taron kasashe masu amfani da harshen faransanci karo na 16 a Madagascar
Taron kasashe masu amfani da harshen faransanci karo na 16 a Madagascar GIANLUIGI GUERCIA / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

A gobe Asabar ake soma babban taron kasashen dake amfani da harshen faransanci karo na 16 a karkashin Shugabancin sakatariyar Kungiyar Michaelle Jean a kasar Madagasacar. Shugabanin kasashe kusan 30 ne za su halartar wannan taro da ake sa ran zai fi maida hankali kan batutuwan da suka shafi yan gudun hijira. 

Talla

A jajuburin soma babban taron kasashe masu amfani da harshen Faransanci a birnin Antannanarivo babban birnin kasar wannan gangami zai maida hankali kan batutuwa da suka shafi makomar kasashen dama yanayi yan gudun hijira musaman yi amfani da wannan dama domin isar da kira zuwa kasashe domin baiwa yan gudun hijira mazauni.

Sakatariyar kungiyar kasashen dake amfani da harshen Faransaci OIF Michaelle Jean ta bayyana cewa cikin dan karami lokaci ya dace kasashen masu hannu da shuni sun mayar da hankali kan wannan bala’i wanda ya tilasatawa da dama barin matsugunin su ,yayinda wasu mutanen suka kasasance a matsayin yan gudun hijira da kuma ke neman agaji domin tsira da mutuncin su .

Sama da shugabanin kasashe 30 ne za su kasancewa a wannan gangami na Antananarivo daga cikin mayan bakin akwai Shugaban Faransa Francois Hollande wanda shaka babu zai haduwa da Ali Bongo Ondimba na kasar Gabon .
Manufar wannan taro a dai bangare shine na yi amfani da harshen faransanci a matsayin gada domin bunkasa kasashen tsakanin su dama karfafa huldar diflomasiya a baki daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.