Najeriya

An bukaci yin aiki da dokar auren wuri a Najeriya

Ana aurar da Mata kafin shekaru 18 a Najeriya
Ana aurar da Mata kafin shekaru 18 a Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye

Kungiyoyin Kare hakkokin mata a Najeriya sun bukaci gwamnatin kasar ta gaggauta daukar matakan hana aurar da mata da wuri bayan kasar ta amince da shirin kungiyar kasashen Afirka na yaki da auran wuri.

Talla

Wannan ya biyo bayan kaddamar da shiri na musamman da gwamnatin kasar ta yi domin kare hakkokin mata da kuma aiwatar da dokar da za ta hukunta masu tilasta musu auran.

Gwamnatin Najeriya ta amince da dokar hana aurar da mata da wuri a shekarar 2003, amma ya zuwa yanzu Jihohi 23 kawai suka aiwatar da dokar.

Hukumar UNICEF ta ce akalla ‘yan mata 4 daga cikin 10 ake aurar da su kafin su kai shekaru 18 a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.