UN

Amina Muhammad ta zama mataimakiyar Sakatare Janar na MDD

Ministar Muhallin Najeriya Amina Muhammed ta zama mataimakin sakatare janar a MDD
Ministar Muhallin Najeriya Amina Muhammed ta zama mataimakin sakatare janar a MDD

Sabon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya zabi Ministar Muhalli a Najeriya, Amina Muhammad, a matsayin mataimakiyar sa, tare da nada wasu mata biyu a wasu manyan mukamai a Majalisar.

Talla

Mista Guterres da wa’adinsa ke soma wa daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa, ya mayar da hankali sosai wajen daidaito tsakanin maza da mata a majalisar.

Babbar Jami'a a ma'aikatar harkokin ketaren Brazil, Maria Luiza Ribeiro Viotti ce za ta rike mukamin shugabar ma'aikata a ofishin sabon sakataren, yayin da Kyung-wha daga Koriya Ta Kudu, za ta kasance a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan tsare-tsare.

Dama an yi ta rade-radin cewa za a nada Amina Mohammed a wannan mukami sakamon rawar da ta, ta ka wajen jagorantar yarjejeniyar sabbin muradun karni na ci gaba mai dorewa da aka kulla don kawar da talauci kafin shekara ta 2030.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.