Libya

Fararen hular da aka tsare a Sirte na bukatar taimako

Sojoji masu biyayya ga gwamnatin Libya
Sojoji masu biyayya ga gwamnatin Libya REUTERS/Ismail Zitouny

Kungiyar kare hakkin dan’adam ta Human Rigts Watch, ta bukaci gwamnatin Libya ta kare mutuncin fararen hular da aka tsare, wadanda sojin kasar suka kame bayan kakkabe mayakan IS daga birnin Sirte, bisa zarginsu da alaka da mayakan.

Talla

Kungiyar ta ce sama da mata da kananan yara 120 da ake tsare da su a gidan yarin Misrata ne ke bukatar agajin gaggawa na abinci da magunguna.

Wani jami’in kula da gidan yari a kasar ya ce, da dama daga cikin matan da kananan yara da ke tsare basu da shaidar zama ‘yan kasar, yayinda wasu kuma akwai yiwuwar mayakan na IS sun sace su ne da nufin yin garkuwa da su, kafin korar mayakan da sojin kasar suka yi da daga birnin na Sirte.

A ranar 5 ga watan Disamba da muke ciki, sojin gwamnatin hadin kan Libya ta sanar da samun nasarar murkushe mayakan IS tare da karbe birnin Sirte daga hannunsu, bayan shafe watanni 8 suna fafatawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.