DR Congo

Kabila ya amince da mika shugabanci a karshen 2017

Limaman Katolika masu shiga tsakani a Kinshasa, 31 disemba 2016.
Limaman Katolika masu shiga tsakani a Kinshasa, 31 disemba 2016. REUTERS/Thomas Mukoya

Bangaren gwamnati dana jam’iyyun adawa a jamhuriyyar Congo sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta kawo karshen takkaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu da ta haifar kazamin rikici a sassan kasar.  

Talla

Karkashin yarjejeniyar dai shugaba Kabila zai ci gaba da jagorancin kasar zuwa karshen shekara ta 2017, za’a kuma kafa kwamitin tsara karbar mulki karkashin jagoran ‘yan adawar kasar Etienne Tshisekedi.

Zalika karkashin yarjejeniyar, dole ne a Joseph Kabila ya mika mukamin Firaminista ga bangaren ‘yan adawar kasar.

Da farko dai cijewar da bangarorin biyu suka yi ya sa, a jiya juma’a kungiyar limaman na Katolika ta yi barazanar kawo karshen shiga tsakanin da take yi a yau assabar, ko an cimma yarjejeniya ko ba a cimmata ba.

Bayan da shugaban limaman na katolika dake shiga tsakani , Mgr Marcel Utembi, ya dora alhakin rashin cimma kan bangarorin biyu da yace don bukatun kansu sun yi garkuwa da alummar kasar ta Congo.

An dai fara wannan tattauanawa ne a ranar 8 ga wannan wata december, bayan da shugaban kasar Josef Kabila dake kan mulki tun cikin 2001 ya ce ba zai sauka daga kan mulkin kasar ba, sai an kara masa wasu shekarun nan gaba.

Kawo yanzu dai mutane sama da 30 suka rasa rayukansu a kasar sakamakon taho mu gamar da ake ci gaba da yi tsakanin yan adawa masu zanga zangar kin amincewa da matakin tazarcen na shugaba Kabila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.