Amb. Sherif kan rantsar da Akufo-Addo na Ghana
Wallafawa ranar:
Sauti 03:09
An shirya rantsar da sabon shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo wanda ya yi nasarar kawar da shugaba mai ci John Dramani Mahama a babban zaben kasar da aka yi a farkon watan jiya. Ambassador Shuaibu Sherif, jigo ne na jamiyyar sabon shugaban kasar NPP, ya shaida wa Garba Aliyu Zarian cewa, sun gamsu da hadin kan da suke samu daga jami'an gwamnatin da za su gada wajen shirye-shiryen mika mulki a karshen mako da ke tafe.