Nijar

Issoufou ya saudaukar da kyautar Mandela ga jami’an tsaron Nijar

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou. AFP/AFP

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou, ke, ya bukaci wadanda ke dauke da makamai domin shiga kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi na ta’addanci su ajiye makamansu sannan su rugumi zaman lafiya.

Talla

Shugaban ya fadi haka ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabin shiga sabuwar shekara.

Shugaban ya yi jinjina ga dakarun kasar da na sauran kasashen kawance dangane da nasarar da suke samu a fada da Boko Haram musamman a yankin tafkin Chadi.

Shugaba Issoufou kuma ya sadaukar da kyautar yabo ta Nelson Mandela da aka ba shi ta tsaro zuwa ga Sojojin kasar wacce ya danganta a matsayin yabo da jinjina ga jami’an na tabbatar da tsaro a Nijar.

“Wannan lokaci ne na farin ciki a game da irin nasarar da muka samu a fadan da muke yi da ‘yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi”

Sannan Shugaban ya bukaci masu dauke da makamai wadanda suka fada tarkon bata na kungiyar Boko Haram da kuma sauran kungiyoyi na ta’addanci, da su ajiye makamansu, a cewar shi za a tabbatar da an kare mutuncinsu tare da ba su damar sake ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.