Kamaru

Kamaru ta ki sakin Ahmed Abba wakilin RFI Hausa

Wakilin sashen hausa na RFI, Ahmed Abba da hukumomin Kamaru suka kame
Wakilin sashen hausa na RFI, Ahmed Abba da hukumomin Kamaru suka kame facebook

Karo na 11 ke nan da kotu a birnin Yaounde na kasar Kamaru ke sake dage shari’ar da ta ke yi wa wakilin Sashen Hausa na RFI Ahmed Abba, inda za a ci gaba da shari’ar a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Talla

A zaman kotun a jiya Laraba, lauyoyin da ke kare Abba, sun bukaci kotun ta yi watsi da rahoton wani bincike da aka ce an yi a cikin kwamfuta da kuma wayoyin salular shi, saboda masu binciken sun gabatar da rahotonsu ne ba tare da sun tattauna koda sau daya da wanda ake zargi ba.

Yau dai watanni 18 ke nan da jami’an tsaron kasar ta Kamaru suka kama wakilin na RFI a garin Moroua, bisa zargin cewa yana da alaka da ‘yan Boko Haram.

Sai dai a tsawon wannan lokaci masu shigar da kara sun kasa gabatar da shaidar da ke tabbatar da zargin da ake ma shi, abin da ya sa hukumar gudanarwa ta gidan Fadio France International ta bukaci hukumomi su gaggauta sakin Abba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI