Najeriya

Kwanaki dubu da sace 'yan matan sakandaren Chibok

'Yan matan makarantar Chibok da Boko Haram suka yi garkuwa da su
'Yan matan makarantar Chibok da Boko Haram suka yi garkuwa da su

A Najeriya kwanaki dubu bayan da ‘yan Boko Haram suka sace su a makarantar sakadaren garin Chibok da ke jihar Borno, har yanzu akwai sauran ‘yan mata 195 da ke ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan bindigar.

Talla

A sakon da ya aike da shi dangane da cika wadannan kwanaki dubu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce har yanzu yana da kwarin gwiwar cewa za a gano sauran ‘yan matan, lura da irin namjin kokokarin da hukumomin tsaro ke yi dangane da haka.

 

A wannan karo, masu fafutukar ganin an ceto 'yan matan na Chibok karkashin inuwar kungiyar BringBackOurGirls, sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Abuja fadar gwamnatin kasar, domin jaddada matsayinsu na ganin an sako sauran dalibai akalla 195 da ke hannun mayakan na Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.