Nijar

Boko Haram ta kashe fararen hula 177 tsakanin 2015 zuwa 2016

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da harin farko a Nijar a watan Fabrairun 2015
Mayakan Boko Haram sun kaddamar da harin farko a Nijar a watan Fabrairun 2015 RFI/Madjiasra Nako

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsakanin watan Fabarairun 2015 zuwa Sataumban 2016, kungiyar Boko Haram ta kashe fararen hula 177 a jihar Diffa da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar.

Talla

Rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a Yamai fadar gwamnatin Nijar ya ce akwai mutane akalla 13 da suka bata yayin da kungiyar Boko Haram ta sace hudu a yankin.
Mutane 101 an kashe su ne a yankin Bosso da ke bakin tafkin Chadi, sai 64 wadanda aka kashe a Diffa sannan wasu 12 a Nguimi.

Rahoton kuma ya ce adadin mutane 137 aka jikkata a hare haren na Boko Haram tsakanin 6 ga watan Fabrairun 2015 zuwa 30 ga SAtumban 2016.

Rahoton dai bai bayar da alkalumman adadin sojojin Nijar da aka kashe ba a hare haren na Boko Haram.

Alkalumman kuma ba su kunshi hare haren da Boko Haram ta kai ba a tsakanin watan Oktoban 2016 zuwa Janairun 2017.

Mayakan Boko Haram na Najeriya sun fara kaddamar da harin farko ne a ranar 6 ga watan Fabrairun 2015 a Nijar. Kuma tun daga lokacin suke kai hare hare a yankin Jihar Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.