COTE D'IVOIRE

Cote d’Ivoire ta cimma jituwa da sojojin da ke bore

Motocin soji a Bouake kasar Cote d'Ivoire
Motocin soji a Bouake kasar Cote d'Ivoire STR / AFP

An cimma jituwa tsakanin sojoji masu bore da kuma gwamnatin kasar Cote D’Ivore, sakamakon wata tattaunawa da aka yi tsakanin ministan tsaro da kuma jagoran masu boren a birnin Bouake da ke arewacin kasar.

Talla

Ministan tsaron kasar Alain Richard ya ce gwamnati za ta biya wa sojojin da bukatunsu da suka hada da samar masu da gidajen da kuma kudaden alawus.

An shafe kwanaki biyu Sojojin na bore wadanda suka kwace ikon birnin Bouake a ranar Juma’a tare da razana mazauna garin da harbin bindigogi.

Mista Richard ya ce tun bara ne gwamnati fara aikin gyre-gyare a cikin barikoki domin inganta rayuwar sojoji. Kuma ya ce za a biya kowa hakkinsa a cikin gaggauwa.

Ministan ya amsa cewa akwai matsaloli da dama da suke fuskanta a fagen aiki, saboda haka ne suka amince da yin tattaunawa da sojojin domin samar da maslaha.

Sannan ya ce za su cika dukkanin alkawullan da gwamnati ta dauka amma idan Sojojin sun ba suu tabbacin haka.

“Ina sanar da al’umma cewa sojojinmu ba su da wata mummunar manufa, sun fito ne domin bayyana damuwarsu, mun fahinci abinda ke damun su, kuma za mu isar da sakonsu ga shugaban kasa” a cewar ministan na tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.