Chad

Habre zai kalubalanci hukuncin daurin rai da rai

Tsohon Shugaban Chadi Hissène Habré
Tsohon Shugaban Chadi Hissène Habré FILES / AFP

Kotu ta musamman a birnin Dakar na kasar Senegal za ta fara sauraren karar da tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habare ya daukaka bayan yanke ma shi hukuncin dauri biyo bayan samun sa da laifufukan yaki da cin zarafin bil’adama lokacin da ya ke mulki.

Talla

Kotun musamman da kungiyar Tarayyar Afirka ta kafa, ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ne akan tsohon shugaban kasar ta Chadi, tare da biyan kudin tara yuru dubu 30 ga kowane daga cikin mutane sama da dubu 40 da aka azabtar lokacin mulkinsa.

Amma tsohon shugaban ya daukaka kara domin kalubalantar hukuncin bayan ya ki amincewa da halaccin kotun.

A yau Litinin ne kuma lauyoyinsa za su fara kare shi a zaman kotun da za a dauki kwanaki ana shari’a har zuwa 30 ga Afrilu inda kotun za ta zartar da hukunci.

Hukuncin da kotun daukaka karar za ta yanke, zai kasance na karshe, idan kuma ta amince da hukuncin da aka yanke wa Habre, ya zama wajibi ya je gidan yari a Senegal ko a wata kasa da ke cikin kungiyar Tarayyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.