ECOWAS-GAMBIA

Tawagar Ecowas za ta sake ganawa da Jammeh

Shugaban Gambia da ke nuna turjiyar sauka daga mulki duk da shan kaye a zabe Yahya Jammeh
Shugaban Gambia da ke nuna turjiyar sauka daga mulki duk da shan kaye a zabe Yahya Jammeh ISSOUF SANOGO / AFP

Kungiyar kasashen yammacin Afirka Ecowas-Cedeao ta yanke shawarar sake tura wata tawaga da za ta kunshi shugabannin yankin zuwa birnin Banjul domin ganawa da shugaban Gambia mai barin gado Yahya Jammeh, a kokarin shawo kansa ya amince da shan kaye a zaben kasar.

Talla

Taron shugabannin kasashen yankin da aka gudanar jiya litinin a birnin Abuja ne ya yanke wannan shawara, kuma a gobe ne tawagar za ta gana da Jammeh.

Matakin da ke biyo bayan ko-in-Kulla da barazanar kungiyar da Jammeh ya nuna kan sauka daga mulki.

A ranar 18 ga watan Janairu Wa'adin Jammeh ke karewa kuma ake saran Zabebben Shugaba Adama Barrow ya karbi rantsuwar kama aiki.

Ecowas na bayyana furgaban ta kan halin da Gambia za ta tsinci kan ta a ciki Muddin Lokacin Jammeh ya cika bai bar karagar mulki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.