Bakonmu a Yau

Dr. Jibrin Ibrahim kan rikicin siyasar Gambia

Shugaban Gambia Yahya Jammeh
Shugaban Gambia Yahya Jammeh

Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika sun soke kai ziyara a wannan Laraba a kasar Gambia a kokarin shawon kan Yahya Jammeh don ganin ya mika ragamar mulki ga Adama Barrow, in da aka dage kai ziyarar har zuwa ranar juma’a mai zuwa. Sai dai shugabannin sun ce, batun ganin ya mika mulkin na nan daram. Wannan kuma na zuwa ne a wani lokaci da babban mai sharia na kasar Emmanuel Fagbenla ya sanar cewa, a cikin watan biyar ko na sha-daya za su saurari batun makudi da Yahya Jammeh ya ce an yi a zaben. Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dr. Jibrin Ibrahim masanin harkokin siyasar Afrika kan wannan dambarwa ta Gambia.

Talla

Dr. Jibrin Ibrahim kan rikicin siyasar Gambia

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.