Najeriya

Majalisar Dattijai ta bukaci a janye dokar haramta shigo da motoci

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki ynaija.com

Majalisar dattijai a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Tarayya ta janye dokar haramta shigo da motoci ta kan iyakokin kasar da ta soma aiki tun a 1 ga watan Janairu. Dubban mutane za su rasa ayyukan yi sakamakon daukar matakin, a cewar Majalisar.

Talla

Wasu Senatocin arewa ne suka gabatar da kudirin inda suka yi watsi da matakin haramta shigo da motocin ta kan iyakokin Najeriya na kasa.

Senatocin sun hada Shehu Sani daga Jihar Kaduna da Kabiru Gaya daga Jihar Kano wadanda suka danganta daukar matakin a matsayin rashin adalci ga Talakawa da ke cin abinci ta hanyar sana’ar Mota.

Sanata Kabiru Marafa daga Jihar Zamfara ya shaidawa RFI Hausa cewa gwamnati na iya saka haraji ga ‘Yan fito amma ba daukar matakin haramta shigo da motocin ba.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattijan da ya jagoranci zaman Majalisar a yau Laraba ya yi kira ga gwamnatin Buhari ta diba koken na ‘yan Najeriya. Sannan Majalisar ta bukaci kwamitin kula da ayyukan fasa kwabri ya gudanar da bincike kan dalilan da har ya sa aka dauki matakin haramta shigo da motocin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.