Cote d'Ivoire

A karon farko an nada mataimakin shugaban kasa a Cote d'Ivoire

Sabon mataimakin shugaban kasar Cote d'Ivoire Kablan Duncan.
Sabon mataimakin shugaban kasar Cote d'Ivoire Kablan Duncan. AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO

An rantsar da Kablan Duncan a matsayin mataimakin shugaban kasar Cote d’Ivoire wanda shine  karo na farko da aka samu mataimakin shugaba kamar dai yadda sabon kundin tsarin mulkin kasar ya shata.

Talla

Duncan mai shekaru 73 a duniya, kafin ba shi wannan matsayi, yana rike ne da mukamin firaminista a karkashin gwamnatin Alassan Ouattara.

A yayin rantsar da Duncan ya yi alkawarin aiki da shugaba Ouattara don ganin kasar ta fice daga cikin kangin da ta fada.

Cote d’Ivoire mai arzikin cocoa ta sha fama da rikici musanman a shekarar 2002, rikicin  da ya yi sanadiyar rayukan mutane da dama tare da  gurgunta tattalin arzikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.