Masar

Kotun Masar ta hana mekawa Saudiya wasu tsibirai guda 2

Tsibiran Tiran da Sanafir da ake takandama a tsakanin Saudiya da Masar.
Tsibiran Tiran da Sanafir da ake takandama a tsakanin Saudiya da Masar. STRINGER / AFP

Wata kotu a Masar ta hana gwamnatin kasar mekawa Saudiya wasu tsibirai biyu bisa yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla a baya.

Talla

Alkalin kotun ya ce an zartar da hukuncin ne saboda cewa tsibiran 2 da suka hada da Tiran da Sanafir sun kasance mallakin kasar Masar ne.

A watan Afrilun bara ne Shugaba Abdel-fatah al-Sisi ya amince tare da sanya hannu kan yarjejeniya mekawa Saudiya tsibiran da yace mallakin kasar ne da farko.

A watan Afrilun bara kasashen biyu suka cimma yarjejeniya na sake meka wa Saudiya ikon tsibiran biyu da dama Masar ta bata a matsayin jingina a shekarar 1950.

Tun bayan kulla yarjejeniyar dai an sami barkewar zanga-zanga na masu adawa da matakin gwamnati, inda aka tsare mutane fiye da dari.

Sai dai a yau litinin ne kotu ta yanke hukuncin al’amarin da ke zuwa bayan da Gwamnatin shugaba Abdel-Fatah al-Sisi ta meka kokenta gaban majalisa don samun amincewarta kan bai wa Saudiya ikon Tsibiran biyu.

A yayin da alkali ya zartas da hukuncin dai lawyoyi da masu rajin kare hakkin dan adama da ke cikin kotu da yawancinsu ke adawa da matakin na gwamnatin sun yi ta bayyana farin cikinsu da hyukumcin na kotu, suna ihun murna tare da bayyana cewa tsibiran mallakin kasarsu ta Masar ne.

Ana ganin kin mekawa Saudiya iko da tsibiran 2 al’amari ne da zai kawo koma baya ga huldar da ke a tsakanin kasashen biyu

Akwai kuma fargabar janye tallafin kudin da Saudiya ta dadde tana bai wa gwamnatin shugaba alSisi tun bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi a shekarar 2013.

Gwamnatin Masar dai na da damar kalubalantar hukuncin na yau ta hanyar daukaka kara a kotun gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.