Zimbabwe

‘Yan sanda sun cafke Faston da ke hasashen mutuwar Mugabe

‘Yan Sandan kasar Zimbabwe na tsare da wani shugaban Chochi a kasar wanda ya ce shugaba Robert Mugabe na iya mutuwa cikin watanin 10 masu zuwa.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe Reuters/Philimon Bulawayo
Talla

Lauyan Faston Gift Mtisi ya ce Patrick Mugadza na tsare ne a birnin Harare kuma har an gurfanar da shi gaban wata kotun Majistare inda ake zarginsa da laifuka barkatai.

Baya ga laifin sanar da cewa shugaban kasar zai mutu a watan Oktober 2017, ana kuma tuhumar Faston da sanya tufafi masu kama da tutar kasar.

A makon jiya ne dai Faston ya fadawa manema labarai cewa shugaban kasar na su zai mutu a ranar 17 ga watan 10 na wannan shekara.

A watan gobe ne dai shugaba Robert Mugabe ke cika shekaru 93 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI