Mali

Mutane 40 sun mutu a harin bam a Mali

Wasu daga cikin sojojin Mali da ke sintiri a Gao
Wasu daga cikin sojojin Mali da ke sintiri a Gao

Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota makare da bama-bamai a wani sansanin soji da ke birnin Gao na Mali.

Talla

An kaddamar da farmakin ne da misalin karfe 9 na safiyar yau agogon kasar, yayin da motocin daukan mara lafiya da jiragen sama masu saukar ungulu suka isa wurin da lamarin ya faru don bada agaji.

Sansanin dai na kunshe da dakarun gwamnati da kuma mambobin kungiyoyin ‘yan adawa masu dauke da makamai da ke sintirin hadin gwiwa don magance rikicin yankin arewacin Mali kamar yadda suka cimma matsaya a yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.