Gambia

Kungiyoyin kare hakkin dan'adam sun bukaci a hukunta Jammeh

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Dakar na Senegal.
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Dakar na Senegal. REUTERS/Sophia Shadid

Wasu kungiyoyin kare hakkin dan’adam, sun bukaci da a kama, tare da hukunta Yahaya Jammeh bisa zargin da ake masa na tsare masu adawa da gwamnatinsa, hadi azabatar da su.

Talla

To sai dai shugaban Gambia Adama Barrow ya bukaci da a bi komai a sannu, bayan wallafa bukatar soke shirin bawa Jammeh mafaka da wasu kungiyoyin kare hakkin dan’adam suka yi shafin internet.

Yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na AP, Adama Barrow ya ce, zai fi kyau da fari a kafa hukuma ta musamman, da zata gudanar da sahihin bincike bisa zargin da akewa Jammeh, kafin daukar matakin da ya dace.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ‘yan kasar Gambia 46,000 suka tsere zuwa Senegal, bisa fargabar barkewar rikici, bayan da Yahya Jammeh ya ki amincewa ya sauka daga mulki a wanccan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.