Gambia

Jammeh ya wawushe dukiyar Gambia

Yahya Jammeh ya samu mafaka a Equatorial Guinea
Yahya Jammeh ya samu mafaka a Equatorial Guinea REUTERS/Thierry Gouegnon

Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh ya batar da miliyoyin dalolin kasar kafin ya tsallaka ya fice, kamar yadda wani Jami’in sabon Shugaban Gambia Adama Barrow ya tabbatar.

Talla

Mai Ahmed Fatty mai ba Adama Barrow shawara ya ce Jammeh ya kwashe dukiyar Gambia da wasu motocin alfarma.

Jami’in ya ce a cikin makwanni biyu, tsohon shugaban kasar ya kwashe Dala miliyan 11 daga baitulmalin Gambia.

Fatty ya ce yanzu haka babu sisin kwabo a cikin asusun ajiyar kasar, yayin da aka nemi wasu motocin alfarmar gwamnati aka rasa.

A ranar Asabar ne Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 yana mulki a Gambia ya fice zuwa kasar Equatorial Guinea inda ake tunanin zai ci gaba da rayuwa da iyalan shi.

Tuni dai sojojin kasashen Afirka ta Yamma suka mamaye sassan birnin Banjul domin tabbatar da zaman lafiya kafin isar sabon shugaban kasar Adama Barrow daga Senegal inda aka rantsar da shi.

Bayanai masu karo da juna na cewar, akwai wata yarjejeniya da aka tsara da za ta hana binciken tsohon shugaban amma ministan harkokin wajen Senegal ya ce ba shi da masaniya akai.

Wasu mutane sun fara sukar yarjejeniyar da ta bayyana cewar gwamnatin Gambia ba za ta dauki wasu matakan da za su ci zarafin tsohon shugaban ba ko kwace ma shi kadarori ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.