Sudan

Jagoran Adawa Mahdi ya dawo Sudan

Tsohon Firaministan Sudan Sadiq al-Mahdi
Tsohon Firaministan Sudan Sadiq al-Mahdi Reuters/Zohra Bensemra

Shugaban ‘yan adawa kuma tsohon Firaministan Sudan, Sadiq al-Mahdi ya koma kasar bayan shafe fiye da shekaru biyu yana gudun hijira a kasashen waje.

Talla

Jam’iyyarsa ta Umma Party ta tabbatar da komawar Mahdi, wanda aka yi wa gwamnatinsa juyin mulki a shekarar 1989, abin da ya bai wa shugaba Omar al-Bashir damar darewa kan karagar mulki.

‘Yar tsohon Firaministan Mariam Mahdi kuma shugabar Jam’iyyarsa ta adawa Umma, ta ce gwamnati ta harmatawa dubban magoya bayan shi zuwa tashar jirgin sama domin tarbon shi.

A shekarar 2014 ne ya fice Sudan bayan sakin shi daga daurin talala akan zargin da ake ma shin a cin amanar kasa.

An cafke shi ne bayan ya zargi dakarun gwamnatin al Bashir da aikata fyade da cin zarafi a yankin Darfur.

Al Kasoum AbdulRahman masani siyasar Afrika yana ganin dawowar Mahdi na da tasiri ga sauya siyasar Sudan duk da barazanar dauri da ya ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.