Najeriya

Najeriya: Buhari na nan cikin koshin lafiya

shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP PHOTO /STRINGER

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da jita-jitar da ake rurutawa cewar shugaban kasar Muhammadu Buhari na fama da tsananin rashin lafiya bayan ya tafi hutu a London. Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ya ce labarin kanzon kurege ne daga bakin wadanda ba su nufin Najeriya da alheri.

Talla

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake wa Shugaban mummunar fata, wanda ko a makon jiya sai da mai Magana da yawun shugaban Garba Shehu ya mayar da martani ga wasu da ke yada jita-jitar cewar Buhari na cikin mawuyacin hali ko ma ya rasu.

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar hukunta wadanda ke yada jita-jitar akan lafiyar shugaban na Najeriya, musamman wadanda ke yada labarin ta hanyar sako a wayoyin salula da kafofin sadarwa na intanet.

Minsitan yada labaran kasar Lai Muhammed ya ce ana wa shugaban mummunan fata ne saboda ya toshe kafar satar dukiyar kasa

Alhaji Shehu Ashaka dan siyasa a arewacin kasar ya ce Talakan da suka zabi Buhari, su ne za su taimaka wajen ganin ya samu nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.