Congo

Yunkurin dawo da Moroko cikin Kungiyar AU

Taron Kungiyar Tarayyar Afrika zai mayar da hankali kan rikicin Libya da mayar da Moroko cikin kungiyar.
Taron Kungiyar Tarayyar Afrika zai mayar da hankali kan rikicin Libya da mayar da Moroko cikin kungiyar.

Taron shugabannin kasashen Afirka da aka fara wannan juma’a a birnin Brazzaville na kasar Congo, na tattaunawa ne kan yakin basasar Libya da kuma yunkurin sake dawo da kasar Maroko a cikin kungiyar.

Talla

Akwai shugabannin kasashen Afirka da dama da ke halartar wannan taro a karkashin jagorancin Denis Sassou Ngesso shugaban Congo.

Duk da cewa an kira taron ne domin tattauna halin da ake ciki a Libya, to sai dai ko shakka babu batun sake dawo da Moroko a kungiyar tarayyar Afirka na a matsayin wanda zai mamaye taron.

A ranar litinin mai zuwa ne dai za a fara taron kungiyar ta Afirka a birnin Adis Ababa na Habasha, kuma a lokacinsa ne Maroko za ta gabatar da bukatar sake shiga kungiyar a hukumance.

Maroko dai ta fice daga tsohuwar kungiyar hada kan kasashen Afirka ta OAU ne a a shekarar 1984 bayan da aka amince da yankin Saharawi ya kasance mamba a kungiyar.

To sai dai lura da muhimmancin sabuwar kungiyar Tarayyar Afirka AU, mahukuntan birnin Rabat karkashin jagorancin sarki Muhammad na 6, sun kaddamar da yunkuri irin na diflomasiyya domin ganin cewa kasar ta gaggauta komawa a cikin kungiyar lokacin wannan taronta da za a fara a ranar litinin ta makon gobe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.