Madagascar

'Yan rakiyar amarya 47 sun mutu a hadarin mota

Mutane fiye da 40 ne suka mutu a hadarin da ya rutsa da 'yan rakiyar amarya.
Mutane fiye da 40 ne suka mutu a hadarin da ya rutsa da 'yan rakiyar amarya. Google Maps

Yansanda a kasar Madagascar sun ce yan daukar amarya 47 ne suka mutu lokacin da motar da suke ciki ta fada wani kogi.

Talla

Bayanai sun ce an samu hadarin ne kusa da garin Anjozorobe da ke da nisan kilomita 90 daga birnin Antananarivo, kuma cikin wadanda suka mutu har da yara 10.

Kakakin Yan Sandan Herilala Andrianatisaona ya ce hadari ya ritsa da angon da amaryar sa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.