Sudan ta kudu

Sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu.

Ana zargin 'yan tawaye da tayar da rikici a Sudan ta Kudu.
Ana zargin 'yan tawaye da tayar da rikici a Sudan ta Kudu. REUTERS/James Akena

Rahotanni daga Sudan ta kudu sun ce an samu barkewar tashin hankali a Malakal, birni na biyu mafi girma a kasar kuma cibiyar hakar man fetur.

Talla

Kakakin sojin Sudan ta kudu Kanar Santo Domic Chol ya ce ‘Yan tawayen sun dadde suna neman tayar da hankali bayan zaman lafiyan da aka samu a Yankin.

Sai dai kakakin ‘yan tawayen Gatjiath Deng ya zargi sojojin ne da kaddamar da haria sansanin su.

Deng ya ce dakarun su sun yi nasarar kassara sojojin gwamnati a karawar da akayi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.