Isa ga babban shafi
AU

AU ta amince da ficewa daga kotun ICC

Shugabannin kasashen Afrika a birnin Addis Ababa na Habasha
Shugabannin kasashen Afrika a birnin Addis Ababa na Habasha AFP/Zacharias ABUBEKER
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

An Kammala taron shugabanin kungiyar kasashen Afrika ta AU a birnin Addis Ababa na Habasha, in da shugabanin suka amince da shirin janyewa daga kotun duniya ta ICC saboda abin da suka kira rashin adalcin da ta ke yi wa shugabanin Afrika.

Talla

Kungiyar ta yi korafi kan matakan da kotun ta dauka kan shugabanin kasashen Sudan Omar Hassan al Bashir da kuma na Kenya Uhuru Kenyatta.

Taron ya kuma amince da mayar da kasar Morocco a matsayin wakiliya da kuma shirin rage dogaro da tallafin da kasashen Afrika ke samu daga kasashen duniya.

Kazalika taron ya zabi Moussa Faki Mahamat, ministan harkokin wajen Chadi a matsayin sabon shugaban kungiyar ta AU, in da ya maye gurbin Nkosazana Dlamini Zuma bayan ya doke abokiyar takararsa Amina Mohamed, ministar harkokin wajen Kenya a fafatawar da suka yi a zagaye na karshe don neman babbar kujerar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.