Sudan ta Kudu

Rikici ya sake barkewa a Sudan ta Kudu

Rikici ya sake barkewa a yankin Malakal na Sudan ta Kudu
Rikici ya sake barkewa a yankin Malakal na Sudan ta Kudu REUTERS/Jok Solomon

Rahotanni daga Sudan ta Kudu sun ce, an samu barkewar tashin hankali a Malakal, birni na biyu mafi girma a kasar kuma cibiyar hakar man fetur.

Talla

Kakakin sojin Sudan ta Kudu, Kanar Santo Domic Chol ya ce, 'yan tawayen sun dade suna neman tada hankali bayan zaman lafiyar da aka samu a yankin.

Sai dai kakakin 'yan tawayen Gatjiath Deng, ya zargi sojojin ne da kaddamar da hari a sansaninsu.

Deng ya ce, dakarun sun yi nasarar kassara sojojin gwamnati a karawar da aka yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI