WHO

Cutar Sankara za ta ci gaba da yin barazana

A 4 ga watan Fabrairu aka ware a matsayin ranar yaki da cutar daji ko Sankara, inda ake gangami domin wayar da kai akan illolin cutar a duniya da kuma hanyoyin magance ta.

Cutar Sankarar bakin mahaifa ta fi yin illa ga mata a kasashen kudu da sahara
Cutar Sankarar bakin mahaifa ta fi yin illa ga mata a kasashen kudu da sahara Arto-Fotolia
Talla

Sankara ta kasance cikin manyan cututtukan da ke barazana ga rayukan bil’adama.

Wani bincike da aka gudanar a Birtaniya ya ce za a samu karuwar cutar ga mata da kashi 3 daga nan zuwa shekarar 2035.

Cutar dai ta fi shafar mata a mahaifa da nono, kuma binciken ya ce ta fi kama masu kiba da shan taba da barasa.

Za a yi wa Mata ‘yan shekaru 15 rigakafin cutar Sankarar mahaifa da nono a Nijar

Masana sun bukaci a mayar da hankali ga hanyoyin rigakafin kamuwa da cutar domin kare rayukan miliyoyan jama’a.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce mutane miliyan 14 ake bincikar lafiyarsu duk shekara akan cutar sankara, kuma adadin zai karu zuwa miliyan 21 a shekara ta 2030.

Binciken hukumar kuma ya ce masu fama da cutar da kuma gwamnatoci na kashe kudi da ya kai dala biliyan 107 duk shekara wajen hidima da sayen magungunan cutar sankara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI