Isa ga babban shafi
Kenya

Manoma da makiyaya sun yi rikici a Kenya

Tsananin fari ya haddasa rikicin manoma da makiyaya a yankin arewacin Kenya
Tsananin fari ya haddasa rikicin manoma da makiyaya a yankin arewacin Kenya screammie.com
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 1

Tsananin fari da rashin abincin dabbobi sun haifar da kazamin tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma a yankin arewacin Kenya, lamarin da ya kai ga hallaka mutane 11. 

Talla

Satar shanu da fafutukar samun wurin kiwon dabbobi sakamakon karancin ruwan sama da kuma rikicin siyasa tsakanin shugabanin yankin, na daga cikin matsalolin da suka addabi arewacin na Kenya.

Francis Narunbe, Sarki ne a kbailar Turkana, ya ce sun dade suna fuskantar fari a yankin kuma suna zaman lafiya da makwabtansu, amma 'yan siyasa na amfani da halin da ake ciki wajen raba kan al’umma.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.