Nijar
An yi zanga-zangar adawa da gwamnati a Nijar
Dubban mutane ne suka fito zanga-zanga a Yamai babban birnin Jamhuriyyar domin adawa da tsadar rayuwa da kuma gwamnatin Mahamadou Issoufou. ‘Yan adawa da kungiyoyin fararen hula da malamai da daliban makaranta da ‘yan kasuwa ne suka shiga zanga-zangar ta lumana a Yamai.
Wallafawa ranar:
Talla
Zanga-zangar kuma ta shafi yin adawa da girke dakarun kasashen Faransa da Amurka da Jamus wadanda suka kafa sansanoni a Nijar domin yakar ‘yan ta’ada a Libya da kuma Mali.
Zanga-zagar dai ta yi karo da wadda aka gudanar a watan Janairu domin nuna goyon baya ga gwamnatin Mahamadou Issoufou.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu